HAUSA

Kasafi 2024: Majalisar Zartaswa a Adamawa ta amince akan N225.8bn

Daga: Zakariyya Aliyu Gwaram

A ranar Laraba Majalisar Zartaswa a Jihar Adamawa ta amince da Naira Biliyan Dari Biyu da Ashrin da Biyar da Miliyan Dari Takwas a matsayin kasafin kudin Gwamnati na shekara 2024.

Haka ya biyo bayan zaman Majalisar da Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya jagoranta a gidan Gwamnati Yola.

 

Kasafin da aka masa taken “Kasafin Gyra” a cewar Kwamishinan Labarai, Mrs. Neido G Kofulto bayan zaman Majalisar an kirkiro ne domin magance kalubalen Alummar Jihar Adamawa.

Mrs. Kofulto ta jaddada cewa Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri yayi damarar bunkasa Jihar Adamawa, alummarta da tattalin arziki jihar.

 

Hakazalika,Kwamishinan Kasafi da tsare-tsare Mr. Emmanuel Piridimso yace kimanin Naira Biliyan Dari da Goma Sha uku da Miliyan Dari uku an ware ne wa cefane sannan Biliyan Dari da Goma sha Hudu da Miliyan Dari Biyar an kayyade wa ayyuka.

Acewar Kwamishinan sun kammala komai akan kasafin yayin da suke shirin gabatar da kasafin wa Majalisar Jihar Adamawa ranar Jumma’a.

About the author

Zakariyya Aliyu Gwaram

Official Website of NAS FM Yola 89.9.

Leave a Comment