HAUSA

Gwamnan Fintiri ya Kaddamar da Aikin samar da Kebabbun Gandun Dajin Kiwo a Gongoshi.

Daga Zakariyya Aliyu Gwaram

Gwamnan Jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ya kaddamar da Aikin samar da Kebabbun Gandun Dajin Kiwo karkashin tsarin Ma’aikatar kula da Dabbobi ta Kasa a Gandun Dajin Gongoshi dake Karamar Hukumar Mayo-Belwa.

Tsarin zai yi yinkurin samar da Murabba’in fili talatin wa Makiyaya 32 inda kowannen su zai kula da dabba daya da wanda za’a bai ma horo mutum daya.

Gwamna Fintiri ya jaddada cewa shirin na Hukumar kula da Dabobi da kasa zai taimaka wajen kawo karshen rikice-rikicen manima da makiyaya sannan ya inganta harkan noma kamar kiwon kifi,kula da gandun daji,ruwa da kasan noma. Kamar yadda yayi daidai da tsarin Gwamnati mai ci na tafiya tare da kowa,Gwamnati ta samar da Ofishin kula da dabbobi na jiha domin daidaito a aikin da na tarayya.

Gwamanan ya zayyano wasu karin ayyuka da suka hada da shirin tallafawa wa kasuwancin noma na Gwamnati da kuma dawo da yin rigakafi wa dabbobi.

Ya nuna godiya wa Ma’aikatun kula da dabbobi a matakin jiha da tarayya bisa hobbasaswar su sannan yayi fatan a samu hakan a sauraron bangarorin jihar.

Farfesa Ambrose Voh Shugaban Ofishin Ma’aikatar kula da dabbobi a jihar Adamawa yace shirin na Ma’aikatar tarayya an shake shekaru goma ana kai tare da fatan kawo karshen yawon makiyaya ta hanyar amfani da kiwon zamani da zai samar da ruwa da abincin dabbobi.

Sarkin Garin Dikon dake yankin,Alhaji Ardo Bamanga ya bayyana jin dadin sa da ba da tabbacin cewa makiyaya za su kula da abun da aka samar musu.

Aikin anyi masa taken “Sauya Yanayin Muhalli a jihae Adamawa ta hanyar amfani da shirin Ma’aikatar kula da dabbobi.

About the author

Zakariyya Aliyu Gwaram

Official Website of NAS FM Yola 89.9.

Leave a Comment