HAUSA

Fintiri ya Jaddada damarar Gwamnatinsa don Yaki da Cin Zarafi.

Daga Zakariyya Aliyu Gwaram

Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umar fintiri ya kara tabbatar da aniyar Gwamnatin sa na yakar dukkanin nau’ukan cin zarafin mata a jahar, a woni jawabi da gwamnan yayi wanda yayiwa take da ya’ya mata abin alfaharin mu, gwamnan ya ce gwamnatin sa ta magance dukkanin ababe ke haddasa cin zarafi gwamna fintiri ya kuma yaba da yadda ake samun ci gaba bangaren dokoki musamman wajen samar da ilimi ga ya’ya mata .

Gwamnan Ahmadu Umaru fintiri wanda ya samu wakilcin seketaren gwamnatin jahar Adamawa Barr Auwal D Tukur yayin rufe woni taro na kwanaki goma sha shida da aka shirya domin fadar kar da al’umma kan yadda za’a yaki cin zarafi ,wanda ma’aikatar mata da samar da ci gaba tare da hadin gwiwar abokan hulda suka shirya domin karma wasu fitattun mutane da raja’a wajen yaki da cin zarafi dama karfafawa mata a jahar Adamawa.

Saboda haka Gwamna ya ce gwamnatin sa zata tabbatar an kawo dukkanin nau’ukan cin zarafi tare da hukunta masu aikata laifukan cin zarafi, Fintiri ya bayyana cewa mata na da rawan da zasu taka a dukkanin bangarorin rayuwa, har wayau Gwamnan ya yabawa kungiyoyi masu fafukar kawo karshen cin zarafi a jahar.

Da take magana komishinayar mata da samar da ci gaba Wunfe Anthony ta yabawa Gwamna fintiri da uwar gidan sa Lami Ahmadu fintiri bitsa tsayiwar daka da suka yi wajen yaki da cin zarafi.

Suma a nasu bangaren wakilan kungiyoyin UNFPA da UNDP tare da NCWS sun yaba da shirya taron, sun kuma yabawa gwamnatin jahar Adamawa dama masu ruwa tsaki bitsa gudummawar da suke yi don kawo karshen cin zarafin mata da kanana yara .

Daga cikin wadanda aka karman yayin bikin sun hada, gwamnan jahar Adamawa Ahmadu Umaru fintiri, da mataimakiyarsa Farfesa Kaletapwa farauta wadanda aka zaba a matsayin jakadun yaƙi da cin zarafin mata. Yayin taron an kuma yabawa kakakin majalisar jahar Adamawa Rt Hon Bathiya Wesley da shugaban masu rinjaye na majalisar Kate Mamuno da gudunmawar da suke bawa masu gangamin kawo karshen cin zarafin.

An kuma yabawa hukumomin tsaron da suka hada Hukumar yan sanda Najeriya, da jami’an tsaro farin kaya da rawar da suke takawa wajen yakar dabi’ar cin zarafi.

About the author

Zakariyya Aliyu Gwaram

Official Website of NAS FM Yola 89.9.

Leave a Comment