HAUSA

Gwamna Fintiri yayi maraba da matakin Magance Rikice-rikicen Iyaka.

Gwamnan Jihar Ahmadu Umaru Fintiri ya jaddada aniyar Gwamnatin sa na aiki kafada da Hukumomin da suka dace don tabbatar da magance matsalolin iyaka.

Fintiri yayi wannan furucin ne yayin bude taron kara wa juna sani da Hukumar Sa ido kan Iyakokin Kasa tare da hadin gwiwar Gwamnatin Jihar Adamawa suka shirya a daki taro na Banquet Hall dake gidan Gwamnati Jihar Adamawa a Yola.

Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri yayi godiya da shaida halartan Mataimakan Gwamnanonin Borno,Taraba, Benue, Cross River da Akwa Ibom sannan Shugaban Hukumar sa ido kan Iyakokin Kasa,Mahalarta daga kasashen ketare, Ma’aikatan Gwamnati jahohi da na tarayya.

Gwamnan ya nanata bukatar dake da akwai na samar da kwarya-kwaryan Hukumar Sa ido a Iyakoki sannan ya jaddada muhimmancin ra’ayin mazauna iyaka musamman abun da ya shafi matsuguninsu,damar morar ma’adinai,da kuma basu tsaro wanda suna kunshe cikin makasudin sulhu akan matsalolin iyaka.

A jawabin ta,Shugaban Kwamitin Iyaka a jihar Adamawa kuma Mataimakiyar Gwamnan Jiha Farfesa Kleptawa G. Farauta tace a cikin kadada dubu ashrin da daya na iyaka da Najeriya ke da ahi da kasar Kamaru jihar Adamawa ke da tsawon Kadada 600 wanda ya tsaga K.H 9 a fadinn jihar.

A jawaban su mabanbanta, Shugaban Hukumar Sa ido kan iyakar Kasa Adamu A. Adaji wanda Amina Nyako ta wakilta yayi nunin cewa samar da gamsashen tsaro da zaman lafiya na da alaqa da kyakyawan kula da iyakar kasa. Wakilin Shugabar Hukumar Shige da ficen Kasa yace Najeriya na da akalla kadadar iyaka 712 wanda ba a kange ba.

Taron bitan wanda akayi wa taken “Sauya Iyakoki daga katangar rarrabuwa zuwa gadar hadin kai aikin cigaba” a na saran zai taimaka wajen habaka zaman lafiya, inganta makota da samar da maslaha ta cigaba tsakanin kasashe.

A saurari rahoton a nan:

About the author

Zakariyya Aliyu Gwaram

Official Website of NAS FM Yola 89.9.

Leave a Comment