HAUSA

Gwamna Fintiri Ya Jaddada Hadin kai Da Jihar Taraba Don Dorewar Zaman Lafiya

Daga Zakariyya Aliyu Gwaram

Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya jaddada aniyar sa na aiki kafada da kafada da Jihar Taraba dun ingantanta zaman lafiya sa tsaron alummah.

Gwamna Fintiri yayi wannan furucin ne yayi bude bikin Kamun Kifi na Nwonyo a jihar Taraba.

Bikin Kamun Kifi na Nwonyo yana gudana ne a K.H Ibi na Jihar Taraba, Bikin yakan dauki kwanaki biyu wanda bisa al’ada hakan yake nuna fara Suu ko kuma kafun kifi na shekara.

Ya kunshi wasannin ruwa,wasan Dodo,rawan al’adu sannan Gasan kamun kifi a rana ta biyu.

Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya bayyana bikin a matsayin ginshiki wajen karfafa alaqa tsakanin alummah, da bunkasa hadin kai cikin alummah wanda aka dauki shekaru ana gudanarwa. Gwamnan ya nuna sha’awar hadin gwiwa da Jihar Taraba akan kulla alaqar karfafa zaman lafiya da sauran al’amuran cigaba wanda jahohin biyu za su mora.

Fintiri a saboda haka ya jinjina wa alumman Jikun kan kokarin dorewar zaman lafiya ya kuma yi kira ga shuwagabanni a kowani mataki da su da ge wajen ka re alummah da dukiyoyin su.

Gwamna Agbu kefas na Jihar Taraba yace sun gudanar da Bikin ne don dabbaqa al’adar kaka dakakanni.

Gwamnan ya jaddada aniyar sa na bijiro da ayyukan cigaba a dukkan rassa na Gwamnati da fannin zaman lafiya don jawo masu zuba hannun jari.

Daga cikin masu fada a ji a jihar Taraba Janar TY Danuma mai ritaya ya nuna jin dadin sa bisa kwazo da masu gudanar da Bikin ke nuna wa ya kuma yi kira ga alummah su kasance masu hakuri da junan su.

About the author

Zakariyya Aliyu Gwaram

Official Website of NAS FM Yola 89.9.

Leave a Comment