Breaking News HAUSA

Gwamna Fintiri ya Kaddamar da aikin 14bn don gina Makarantun zamani a fadin Adamawa.

Daga Zakariyya Aliyu Gwaram

Gwamnan Jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ranar Alhamis a Karamar Hukumar Girei ya kaddamar da gina Makarantun zamani a ko wanni karamar Hukumar Jihar Adamawa.

Acewar sa,za a kayatar da Makarantun da dukkan ababen da suka cancanta don ba da ilimi tundaga matakin Nazare,Firamare da Sakandare.

Gwamnan Jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ya bayyana cewa aikin gine-ginen makarantun an samar da isashen fili kuma an ware Biliyan goma sha hudu,da Miliyan Dari Tara da Casa’in da shida, naira dari biyu da tamanin da Takwas da Kobo arbain da bakawai wanda hadakar Gwamnatin jiha da K.H ne zai samar da kudin.

Ana sa ran wannan hadaka ya kawo bunkasar ayyuka a K.H Har ila yau,yin haka yunkurine na Gwamnati ta hanyar amfani da jawaban bukatu da aka tattara na alummar jiha wajen kawo cigaba da yayi daidai da kudirori 8 na Gwamnati mai ci.

Gwamna fintiri yace ba tare da an ruruta ba,cigaban ko wacce alummah ya raja’a ne ga muhimmancin da aka ba wa ilimin yara masu tasowa.

Ya kuma bayyana cewa ilimi na mataki na biyu bayan tsaro a abubuwan da gwamnatin sa ta sa a gaba kamar yadda hakan yayi daidai tsarin Cigaban Karni dama dokar Hukumar ilimi na bai daya UBEC.

Gwamnan Jihar Adamawan har wa yau,ya yabawa cigaban da hadakar zai samar musamman a fannin na ilimi sannan ya sanar da shirin Gwamnati na daukan nauyin karatun mutum 200 a fanni fasaha,kere-kere, da ilimin kirkirarriyar fasaha wato Artificial intelligence a turance,a bisa wannan ya bukaci dukkan Yan asalin jihar da su nade hannun riga don ribatar wannan dama.

A jawaban su mabanbanta Kwamishinan ilimi a jihar Adamawa, Dr. Umar Garba Pella, shugaban Kungiyar K.H ta Najeriya kuma shugaban Karamar Hukumar Song,Alh Abdussalam Gidado da Ibrahim Yayaji Kwamishinan K.H dukkaninsu sun yi amannar cewa wannan yunkuri zai rage yara da ba sa zuwa makaranta ko basu da hanyar samun ilimi wanda hakan zai inganta ribar bil’adama a jihar Adamawa.

A yayin taron Shugaban k.H Girei Juda Amisa,Hakimin Girei Ubandoman Adamawa, Dr. Ahmed Mustafa Ibrahim da ma Dan majalisar jiha a yankin Abubakar Abdullahi sun gabatar da jawaban godiya da san barka.

A saurari rahoton anan;

About the author

Zakariyya Aliyu Gwaram

Official Website of NAS FM Yola 89.9.

Leave a Comment