An watsa Jadawalin Gasar Kwallon Kafa na Hadin Kai da aka fi sani da Pitapwa Unity Football Competition a turance a filin wasa na Makwada a Numan.
Da yake jawabi a yayin watsa jadawalin Gasar wanda ya assasa Gasar Mr. Pitapwa F Vokito ya nanata cewa makasudin shirya gasar shine karfafa hadin Kai da aiki kan manufa guda duk da bambamce bambamce kabilanci, ko addini don cigaban jihar Adamawa.
Mr Pitapwa F Vokito wanda Kwamared Danladi Jonah Shugaban shirya Gasar ya wakilta ya kuma furta cewa aikin jin kan na kunshe da manufar samar da Dandalin dama wa matasa da Allah yayi wa basirar tamola a fadin jihar Adamawa.
Mr. Vokito ya kuma ba da tabbacin yin adalci a gasar kana ya shaida cewa za su bibiyi alkalancin Gasar da ma sha’ani wadan da suka daura don gudanar da Gasan don cimma abun da aka kudirta. Ya kuma bukaci matasan da za su fafata a Gasar da su nuna hallayan ladabci da bin umarni da akasan Yan kwallo da shi.
Gasar za ta kunshi Kananun Hukumomi 9 da suke kudancin Jihar Adamawa inda aka ware Naira Miliyan Guda wa Kungiyar da za ta lashe Gasar,Naira Dubu Dari Biyar ma wanda ta zo na biyu sannan Naira Dubu Dari Biyu da Hamsin wa Kungiyar da zo na uku.
In ba’a manta ba,a shekarar da ta gabata ne aka fara Gasar Kwallon Kafa na Hadin kai a jihar Adamawa wato Pitapwa Unity Football Competition a turance wanda a lokacin Mai horas da kungiyar UB da aka fi sani da Coach Mourinho ya lashe Gasar. Gasar Karo na Biyu a Yankin Kudancin Jihar Adamawa za’a fara ne 4th ga Watan Fabrerun Shekarar da muke ciki inda za’a yaye kallabi da barje gumi a tsakanin Kungiyar Zidon FC da Bandawa United a Filin Wasa na Makwada dake Karar Hukumar Numan.
A saurari Rahoton a nan:
Leave a Comment