Daga Zakariyya Aliyu Gwaram
Saurari rahoto:
Karanta
Gwamnatin Jihar Adamawa na shirin ba da tallafin kudi naira dubu goma-goma wa Matasa da Dattabai ta hannu Hukumar Paweca a fadin jihar nan.
Babban Mai ba da Shawari wa Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri akan Ababen Wallafawa a Kafofin Sadarwa, Ijabani Ijahu shi yayi wannan furuci yayin da ya bayyana a cikin shirin “Safiya Breakfast Show” a Gotel TV.
Mai tallafa wa Gwamnan Kan ababen wallafawa a Shafukan Sadarwa yace a shekarar da ta gabata Gwamnatin Jihar Adamawa ta raba tallafin abinci don rage radadin cire tallafin man petur, ya kuma ja hankalin alummah game da cigaban tallafin Albashi na naira dubu goma da Gwamnati ta ba da na watanni shida.
Yayi tunin cewa, Gwamnatin Adamawa ta kaddamar da Kwamiti da zai yi aiki kafada da Ma’aikatar Kasuwancin Noma na Jihar ADAS-P don samar da iri da kayan noma wa Manoman Rani a wani mataki na tabbatar da wadatan abinci a Adamawa.
Acewar sa,Kafin kwanaki 90 gaba, Gwamnati zata kaddamar da Katafaren Dakin Gwaji da zai kawo karshen zuwa wasu jihohi don neman lafiya.
A bangaren samar da muhalli, Ijabani Ijahu yayi bayanin cewa Gwamnati ta kudirta gina gidaje 2000 don saukaka mallakan muhalli inda ana daf da kammala gidaje 1000 a Malkohi,sannan a yanzu haka ana shirin fara gina sauran.
Ya kuma fayyace cewa gidajen ba wai ma Ma’aikatan Gwamnati kadai bane face dukkan Dan Asalin Jihar Adamawa da yake bukata.
Ijabani yayi kwatance da amincewar kama aiki wa ‘Yan kwangilan gina filin wasa da Gwamnati ke shirin samarwa, gina Kasuwar zamani mai ci ba dare ba rana,sannan amincewa da biyan naira biliyan uku watan da ta gabata don biyan gratuti da pansho a matsayin manuniya ga irin kimtsuwar Gwamnati mai ci wajen kawo cigaba a jihar nan.
Leave a Comment