Trending

Kwamitin Daidaita Karancin Albashi Arewa maso Gabas Ya Gudanar da Taron Sauraron Jawabai a Yola

Saurari rahoto:

Karanta

Taron Sauraron Jawabai na Kwamitin daidaita biyan karancin albashi shiyyar Arewa maso gabas ya auku a Yola.

Ana sa ran taron zai samar da fahimtar juna da matsaya akan karancin albashin da za’a na biyan ma’aikatan Gwamnati.

Gwamnati da masu ruwa da tsaki sun amince cewa tattaro sahihan bayanai shine hanya kadai da zai kawo kwatantan adalci akan karancin albashin.

A jawabinsa na bude taro,Shugaban Kwamitin kuma Shugaban Kwadigon Najeriya Kwamared Joe Ajero ya koka akan yunwan da jama’a ke fama,sannan ya tsaya kan cewa Gwamnati su ke da mafita akan wannan sha’ani.

A jawabinsa,Gwamnan Jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri wanda Mataimakiyar Gwamna Farfesa Kaletapwa G Farauta ta wakilta ya bayyana Arewa maso Gabashin Najeriya a matsayin zuri’a daya saboda haka dole a hada kai don shawo kan matsalan a yankin.

Har wa yau,Mataimakiyar Gwamnan ta nemi Gwamnonin da su himmatu don yin abun da ya dace.

Gwamna Jihar Bauchi,Bala Abdulkadir Muhammed kuma Mamban Kwamitin daidaita Karancin albashi,ya ba da tabbacin sake duba tsarin albashin sannan ya ba da shawarin sake duba tsarin kasafi.

Wasu daga cikin matsalolin da aka alqantan da halin da ake ciki da su sune,tsadan rayuwa, tabarbarewan tsaro da cire tallafin man petur.

Jihar Bauchi ne ta ba shawarin kaso mafi tsoka,jihar Yobe mafi karanci.

A karshen taron ana sa ran Kwamitin su mika rahoto don daukan matakin gaggawa.

About the author

Zakariyya Aliyu Gwaram

Official Website of NAS FM Yola 89.9.

Leave a Comment