HAUSA

Masarautar Katagum Ta Karrama Kakakin Majalisar Bauchi Suleiman Da Sarrautar “Barden Katagum”

Published by Abdulaziz Ibrahim

A wani mataki na girmamawa da nuna godiya Mai Martaba Sarkin Katagum Alhaji Umar Farouk II ya ba da sarautar “Barden Kudun Katagum” ma Kakakin Majalisan Jihar Bauchi Rt. Hon. Abubakar Y Suleiman.

Wannan karamci manuniyace akan sadaukarwan Rt. Hon. Abubakar Y Suleiman wajen samar da cigaba a jihar Bauchi baki daya.

Mai Dalan Katagum, Kabir Dandubi shi ya mika takardan Shaida,da rawanin sarautar a madadin Mai Martaba Sarkin Katagum.

A lokacin,Kabiru Dandubi a madadin Masarautar Katagum,ya yi na’am da gagarumin gudumawar Kakakin Majalisar Bauchi, Rt. Hon. Abubakar Y Suleiman a bangaren shugabanci da zamantakewa.

Ya bayyana Shugaban Majalisar a matsayin “tubalin riko” wanda ya samu shaidan amana da biyayya.

“..Gudumawar ka abun tinkaho ne kuma ka cancanci wannan sarautar ”

“Wannan Sarauta alama ce ta gaskatawa da baiwar da Allah yayi maka a bangaren kawo cigaba ma alummah”, Acewar MaiDalan Katagum.

A jawabinsa, Rt. Hon. Abubakar Y Suleiman ya nuna godiya da jin dadi wa Masarautar Katagum.

Yace ba shakka wannan sarauta nauyi ne inda ya nanata zage dantse wajen karfafa Masarautar Katagum da samar ababen more rayuwa ma alummah.

“..Lallai wannan sarauta mataki ne na kulla alaqa sakanin Shugabanci da Jama’a baki daya.

“Kuma hakan ya karfafa kudirorin mu na hadin kai da zaman lafiya don cigaba mai dorewa a Jihar Bauchi”,Kakakin Majalisar ya jaddada.

Har wa yau,a cewar Kakakin Majalisan,Masarautar Katagum na da tasiri a tarihin rayuwar sa,musamman garin Azare da yayi rayuwa a ciki.

“..Azare gida ne a wajena. Nayi karatu a nan,na gina iyali anan kuma na kulla alaqa ta mutunci da Jama’a da dama”,acewar sa.

Sannan ya kara da godiya marar misaltuwa da yin adduar dorewar Masarautar Katagum.

Sarautar “Barden Katagum” wani mataki ne na yaba gudumawar Rt. Hon. Abubakar Y Suleiman a baya da kuma kwarin gwiwa don karfafa Masarautar Katagum,da samar da cigaba,a gaba.

Rt. Hon. Suleiman ya jaddada aniyar sa na rikon amana don inganta hadin kai,cigaba da zaman lafiya a fadin Jihar Bauchi.

A karshe wannan mukami na sarautar “Barden Katagum” shaida ce akan jajircewan Kakakin Majalisar Jihar Bauchi, Rt. Hon. Abubakar Y Suleiman sannan zai tabbata cikin tarihi irin hobbasawar sa,da sadaukarwa ma cigaban alummah.

About the author

Abdulaziz Ibrahim

Official Website of NAS FM Yola 89.9.

Leave a Comment