HAUSA

Gwamnatin Adamawa Ta Ware Naira Biliyan 2.94 Don Sake Gina Kasuwar Yola Cikin Watanni 9

Published by Abdulaziz Ibrahim

Daga Zakariyya Aliyu Gwaram

Saurari Rahoto:

Karanta:

Gwamnatin Jihar Adamawa ta dau zimmar farfado da Kasuwar Yola inda a zaman Majalisar Zartaswa karo na Goma sha Biyar,Gwamnatin ta amince da sake gina Kasuwar waki’ar Gobara ta shafa watanni biyar da suka wuce akan Naira Biliyan Biyu da Miliyan Casa’in da hudu.

Da yake jawabi wa manema labarai bayan zaman Majalisar Zartaswan na Jihar Adamawa, Dr. John Dabari yace sabuwar Kasuwan da za’a gina zata kunshi bangarorin shago 69 wanda ana sa ran kammalawa cikin watanni tara da zimmar dawo da hada-hadar kasuwanci a kasuwar dake Yola.

Dabari ya bayyana cewa za’a yi garambawul ma kasuwan inda zata samu tsalelen tsari na zamani da zai rage afkuwar gobara a gaba wanda aka amince kan kudi naira Biliyan Biyu da Miliyan Dari Tara da Casa’in da Hudu.

A wani kauli daga zaman Majalisar, Gwamnatin Jihar Adamawa ta shawarci mazauna hanyoyin ruwa da su kaura don gudun fadawa cikin ambaliyan ruwa da ake fuskanta,wannan ya biyo bayan gargadin da Hukumar Kula da Sha’anin da Magudanun ruwa na kasa tayi game da sa ke ruwa da za’a yi daga ma’adanar ruwa na Lagdo.

Idan ba a manta ba,Hukumar ta sanar da za’a fara sake ruwan ne tun ranar Talata data gabata 17 ga watan Satumba inda hasashe ke nuna za’a iya samun ambaliyan ruwa.

Bugu da kari,Kwamishinan Lafiya a Jihar Adamawa Dr. Felix Tangwami yayi ba’asi dangane da barkewan cutar gudawa,Acewar sa daga cikin mutum 180 da aka yi gwaji don zargin cutar,tuni aka salami 30 daga asibitin Kwararru na jiha.

Izuwa wannan gaba dai Gwamnatin Jihar Adamawa ta nanata matsayarta na cigaba da kare alummar ta sannan ta garegadi makarantu da su bi uamarni da matakan kariya daga ambaliyan ruwa.

About the author

Abdulaziz Ibrahim

Official Website of NAS FM Yola 89.9.

Leave a Comment