HAUSA

Gwamnatin Adamawa Ta Dauki Matakan Gaggawa Don Magance Barazanar Ambaliyan Ruwa da Inganta Kiwon Lafiya

Daga Zakariyya Aliyu Gwaram

A wani mataki na shiri tsaf Majalisar Zartaswa na Jihar Adamawa ta gudanar da zamanta na Karo Sha Hudu inda ta ba da gargadi mai tsauri sannan ta dauki kwararan matakai don magance Ambaliyan ruwa, bunkasa gine-gine da ingana kiwon lafiya.

Gwamnatin Jihar Adamawa da take jajanta ma Gwamnatin Jihar Borno bisa Iftila’in ambaliyan ruwa da ya auku tace ta samu kashedi dangane da tsammanin ambaliyan ruwa a wasu sassa na Jihar Adamawa.

Da yake ganawa da Manema labarai bayan zaman Majalisar Zartaswan,Kwamishinan Labarai a Jihar Adamawa Mr. James Iliya,yace Gwamnati tana gargadi wa mazauna Kananun Hukumomin Madagali, Mubi ta Arewa,Shelleng,Demsa,Numan,Song da Yola ta Arewa da su zamto cikin shirin zuwan ambaliyan ruwa musamman daga ranar 16 ga watan Satumba.

Hukumomi masu ruwa da tsaki sun bukaci mazauna wannan yankuna musamman wadanda suka fi kusa da hanyan ruwa da su kaura zuwa waje mai nisa ko tsibiri bugu da kari makarantun da su ke wadan nan yankuna za su kasance a kulle a wannan lokaci domin kare Dalibai.

Har ila yau,bayan gargadi a kan ambaliyan ruwa,Majalisar Zartaswa na Jihar Adamawa ta amince da kwangilar fadada Magudanar ruwa na Samunaka a wani mataki na magance ambaliyan ruwa ya shafi Babban birnin Jiha da ma sauran sassan Adamawa.

An ba da wannan aiki akan kudi Biliyan uku da digo casa’in da hudu wanda aka ba ma kamfanin Triton Najeriya Limited da wa’adin kammalashi cikin watanni shida.

Wannan aikin Kwangilan ya kunshi tono da gina hanyan ruwa mai tsawon kadada biyu da digo hudu domin ya hadu da magudanar ruwa da ake amfani shi. Yin hakan,wani yunkuri ne da zai hana aukuwan ambaliya.

Majalisar Zartaswan har wa yau ta amince da mika Babban Asibitin Mubi da akayi wa Garambawul zuwa hannun Cibiyan Kiwon Lafiya na tarayya wannan shine karo na biyu da irin haka ta faru baya da aka mika Asibitin Hong ga Cibiyar.

Wannan mataki acewar masana zai kawo ingantaccen kiwon lafiya kusa ga alummah,ka na ya rage bukatar tafiya dogon zongon don jinya da sauransu.

Sannan hasashen Kasafi na 2025 wanda yake kimanin Naira Miliyan Dari Biyu da Sittin da Takwas da digo tamanin da Bakwai Majalisar ta amince dashi, kasancewar ya bi ka’idar jadawalin kasafi na MTEF.

Wannan Kasafi ya raja’a ne da rarraba kudaden ayyuka yadda ya kamata kuma wa sassa da suka fi dacewa domin cigaban Jihar Adamawa.

Da Majalisar ta ke mai da jawabi game da barazanar ambaliyan ruwa da ake fuskanta a jihar tace Gwamnati na aiki kafada da kafada da Hukumar Nazarin Hasashen Yanayi Nimet,Ma’aikatar Muhalli na tarayya da sauran masu ruwa da tsaki sannan Majalisar ta tabbatar da cewa Gwamnatin Jihar Adamawa ta tanadi magunguna,kayan abinci da abunuwan agaji a zaman tsammanin wannan waki’a da ake ciki.

About the author

Zakariyya Aliyu Gwaram

Official Website of NAS FM Yola 89.9.

Leave a Comment