Breaking News HAUSA

Gwamna Fintiri ya sa hannu kan tsarin Wadatar da tsaftataccen Ruwa a Adamawa.

Published by Abdulaziz Ibrahim

Daga Zakariyya Aliyu Gwaram

Gwamnatin Jihar Adamawa ta amince da tsarin samar da tsaftatacce kuma wadataccen ruwa a Kauyuka da karkara dake fadin Jihar Adamawa.

Gwamnan Jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri wanda ya saka hannu kan tsarin yace zai kawo wadatanta ruwa da ya kasance muhimmi a rayuwa da cigaban tattalin arziki.

Gwamnan ya bayyana cewa samar da tsaftataccen ruwa ma alummarsa na cikin kudirin Gwamnatinsa tun wa’adin farko.

Fintiri ya jaddada biyayyar Gwamnati ga abun da tsarin ya kunsa.

A jawabin sa,Kwamishinan Kula da Ruwa a Jihar Adamawa, Audu Ayuba Tanko ya bayyana cewa Gwamna Fintiri ya ba da umarni wa Ma’aikatar ruwa na tabbatar da wadatanta tsaftataccen ruwa bai daya wa alummar Adamawa.

Kwamishinan yace sun dau aniyar cimma wadatar da ruwa mai tsafta daga nan zuwa 2030 a Adamawa.

Audu Ayuba yayi bayanin alfanun tsarin da suka kunshi;fadada romon dimukradiyya ga kauyuka da karkara,dama wa Kungiyoyin kasa da kasa don ayyukan jin kai,da sauran su.

Acewar Kwamishinan, tuni aka ingiza Yan Kwangila don kama aiki a Kananun Hukumomi 8 na jihar nan kuma an ba su wa’adin watanni shida don kammala aikin da zai samar da tsaftataccen ruwa ma alummah.

Audu Ayuba Tanko ya yabawa wa sadaukarwar Gwamna Fintiri na samar da tsare-tsare da suka shafi matsalolin alummah. Kana, ya kirayi jama’a da su kaurace wa barnata kayan Gwamnati musamman na ma aikatan samar da ruwa,a karshe ya jinjina wa Kungiyoyin aikin jin kai USAID da sauran su.

Za a iya sauraron rahoton a nan;

About the author

Abdulaziz Ibrahim

Official Website of NAS FM Yola 89.9.

Leave a Comment