Featured

“KARSHEN TIKA…” Fintiri da Binani.

By Zakariyya Aliyu Gwaram

Bisa hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta yanke na tabbatar da nasarar Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri a zaben Adamawa da ya gudana a shekara ta dubu biyu da ashirin da uku(2023),ya kamata an kawo karshen zancen.
Kamar yadda na ayyana a baya, ɗaukaka karan tamkar shuka dusa ne!.

A yanzu, manuniya ta nuna karara,farillan rashin nasara mudin Aishatu Dahiru Binani ta je ga Kotun Koli.

Hankali kadai ya isheta ta gane masu ingiza ‘Yan neman na goro ne.

Binani ta samu damar rike mutuncinta kafun ma taje gaban Kotun Sauraren korafin Zabe da tuhumar nasarar Fintiri,damar da ta kubuce mata walau sakamakon munanan shawarwari ko ya Allah dogon buri ?

Tattakin da tayi zuwa Kotun Daukaka Kara, ƙara dulmuya tayi cikin laka. Ina ganin in har za taji shawarin makusantar ta masu basira to ina mai yakinin za su fada mata cewa kwarjininta ba kaman jiya ba kuma gaba da santsi.

Kimarta zai ci-gaba da gushewa musamman ta bi sahun marar Dan jagora,Uban korafi Dr. Umar Hardo a kotun Koli.

Kotu ta yanke hukunci kuma ko wani dalili ne ya sa Kotun sauraron Korafin Zabe da Kotun Daukaka Kara suka yanke wannan hukunci ba wani abu bane face tabbatar da an bi abun da Alummar Adamawa suka zaba! Gutsuri tsoma da ‘yan bani na iya a Jami’yyar APC ke yi sun kara munana lamari da nunawa a fili Jami’yyar APC a jihar Adamawa ba wata abu bace fa ce Hujajjen Kwale-Kwale da ke gab da nutsewa.

Gaskiya a fade ta, gurbataccen tunanin da ya haifar da wannan shawarin da tayi ba wani abu ya haifar ba illa “zuba gishiri a Gyambo”.

Nasara da Fintiri ya samu akan ‘Yan wujja-wuajjah” ya kara tabbata m

Zaɓe zagaye na biyu wato Supplementary da aka yi ya ƙara tabbatar da nasarar Fintiri da kuma kawar da yunkurin ƙwace kujerar da karfi ta hanyar magudi, lamarin da ya ci tura!

A wasan Dambe, idan ka ci ƙasa sau uku a karon farko ana kiranshi “Kantap”(Knockout).

Wai shin me yasa Binani ba za ta daina jin shawarwarin Shaho ba ta rungumi ƙaddara?
Shin me yasa “Yan kwadayi ba zasu rabu da ita ta huta? Mun san dalili. Ina ganin duk za mu iya amincewa “taurin kai bai haifar da Ɗa mai ido”
Gwamnati tana ci gaba da biyan bukatun Alummah ainun!
Idan har Binani taci gaba da lalume cikin duhu…

Nayi amannar cewa “BA ZA KU TAƁA IYA HALASTA HARAM BA.

Kushi ne ya rubuta daga Yola,
Zakariyya Aliyu Gwaram ya fassara.

About the author

Zakariyya Aliyu Gwaram

Official Website of NAS FM Yola 89.9.

Leave a Comment