HAUSA Local News

Yolde PATE: Mai Jimila ya karyata bidiyon Aladu na shiga Makabarta da tone kabura.


Warning: Attempt to read property "post_excerpt" on null in /home/tabaraun/nasfm.com.ng/wp-content/themes/voice/template-parts/content.php on line 30
Written by NAS FM Yola

Mai Jimilar  Yolde PATE a K.H Yola ta Kudu a jihar nan,Alh Muhammad Jingi ya karyata bidiyo da wata mai suna Amina Usman tayi take nuna cewa makabartar yankin na halin Allawadai.

A bidiyon wande ke karade kafofin sadarwa na zamani,Amina Usman tayi ikrarin cewa Aladu na shiga makabarta cikin dare da tone kabura sakamakon zuber katangan makwancin goben.

Game da haka a hira da Wakilin Nas fM Tasiu Hassan yayi da Maijimilar  Yolde PATE Muhammad jingi yace,zancenta kagene da ba gaskia ko kadan inda yayi nunin cewa babu lokacin da Aladu suka taba tone kabura a cikin Makabartar.

MAI JIMILLA

Ya yarda cewa bangon ginin akwai tsagu da ramuka wanda yace yanzu haka ana kan gyarawa.

Yayin da yake neman alummah suyi watsi da batun ta,ya kuma bukaci Jami’an tsaro da su gayyace ta don bayyana dalilinta nayi wannan kage.

Alh. Muhammad Jingi,yayi kira ga matar da ta aikata wannan bidiyo da ta janye maganar da neman afuwa sannan ya furta cewa duk wanda ke son ba da guduwa wajen aikin gyaran makabartar ya tuntube shi ko daga cikin masu ruwa da tsakin na yanki.

Leave a Comment