Local News

Ku Bi Diddigin Sakamakon Kotu Don Ku Gano Masu Zagon Kasa Ma Jihar Adamawa -Wugira

By Zakariyya Aliyu Gwaram

Saurari rahoto;

Babban Kotun Tarayya a Abuja ta sallami karar da Jami’in da Hukumar Zabe Mai Zaman kanta Inec ta dakatar ya shigar,Hudu Yunusa-Ari wanda yake neman kariya daga Yan Jarida,garkamewa da muzgunawa daga Jami’an tsaro biyo bayan sanarwa da yayi cewa Yar takarar Jami’yyar APC, Sanata Aishatu Dahiru Binani ta lashe zaben Gwamna a Jihar Adamawa.

Wakilinmu Zakariyya Aliyu Gwaram ya rawaito cewa Hudu Yunusa Ari ya shigar da karar Shugaban Yan Sandan Najeriya,Hukumar Yan Sanda ta Kasa,Shugaban Jami’an Tsaro na Farin kaya SSS,da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta Inec.

In ba a manta ba,Sanarwar da Hudu Ari yayi cewa Binani ta lashe zaben Gwamna a Adamawa kotu ta ce karya doka ne sannan Shugabancin Hukumar Zabe Inec ta soke sanarwar wanda hakan ya karar tabbatar da Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri a matsayin Gwamna a Jihar Adamawa.

Lauyoyin Hudu wanda Jibrin Okutepa ke jagoranta sun ce Hudu ya aikata haka ne sakamakon abun da suka kira barkewar tsaro sannan suka ayyana cewa tun aikata wannan lamari wadanda Hudu ya shigar da Karar su ke cigaba da masa barazana,da gayyan taron Yan jarida wanda suke nunin, an aikata hakan tun gabanin kotu ta dau mataki.

Mai Shariah James Omotosho yayin gabatar da hukuncin yace abun duba cikin karar daya ne,shine shaida akan daya daga ciki wadanda ake karar sun tsaga dokar hakkin Dan Adam da Hudu ke dashi.

Da yake tofa Albarkacin bakinsa Mai ba da Shawari na Musamman wa Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri kan harkokin da suka shafi Jama’a kuma Lauya Barrister Sunday Joshua Wugira yace hukuncin da kotun ta yanke manuniya ne akan karfin dimukradiyya da bin daidai da adalci daga fannin Shariah.

Wugira ya bukaci alummah da su tabbatar da sa ido kan wannan sha’ani don fito da bara gurbi sannan ya kara da cewa Jama’a su cigaba da goyon bayan hukuncin kotu akan Shariah don kare hakkin su da tabbatar da gaskia da adalci.

Mai Shariah Omotosho yayi nunin cewa Hudu ya shigar da karar ne don gudun hukunci akan abun da ya aikata a zaben Gwamna da aka yi a jihar Adamawa.

Saboda haka kotu tayi watsi da karar sakamakon rashin kosashen shaida.
COV

About the author

Zakariyya Aliyu Gwaram

Official Website of NAS FM Yola 89.9.

Leave a Comment